Ziyarar da Mai Martaba Sarkin Dutse yayi a Fadar Sarkin Gumel domin ganin Bikin Sallar Gani na 2024.
Dutse Emirate Council Dutse Emirate Council
276 subscribers
135 views
2

 Published On Sep 22, 2024

DAGA FADAR MAI MARTABA SARKIN DUTSE
LAHADI, 22 SEPTEMBER, 2024 - 19 RAB.I., 1446AH.
Assalamun Alaikum…….

MAI MARTABA SARKIN DUTSE ALH. MUHAMMAD HAMIM NUHU SANUSI CFR ya halarci BIKIN SALLAH GANI A GARIN GUMEL, wadda MAI MARTABA SARKIN GUMEL ALH. AHMED MUHAMMAD SANI II CON ya gabatar da Hawa a ranar Lahadi 19 ga wata Rabi’ul Auwal 1446AH_22 ga watan Satumba 2024.

A duk rana irin ta yau ne a shekara Mai Martaba Sarkin Dutse yake zuwa Fadar Mai Martaba Sarkin Gumel domin yin ziyara kana da kuma taya shi murna irin wannan bukukuwa da suke gudanarwa a Masarautar.

Mai Martaba Sarkin Gumel yaji daɗi sosai ganin irin manya baƙin da suke zuwa domin taya su nuna farin cikinsu.

Mai Martaba Sarki ya samu rakiyar wasu daga cikin ‘yan Majalissar sa daga cikin su akwai Mai Girma Madakin Dutse, Ɗan Masanin Dutse, Sarkin Gabas, Sarkin Fada, Magajin Rafi, Kogunan Dutse, Ɗan Malikin Dutse, da kuma Majidaɗin Dutse da sauran masu rakiyar Sarki.

Allah yataimaki Sarakunanmu ya ƙara musu lafiya da nisan kwana mai amfani.

📸/✍️:
WAZIRIN TAFARKIN DUTSE
CEO; Waziri Studio
Fadar Mai Martaba Sarki

show more

Share/Embed